Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari A Birnin Maiduguri


Nigeria Boko Haram
Nigeria Boko Haram

Shaidun gani da ido a garin Maiduguri dake arewa maso gabashin Nigeriya sun ce ‘yan boko haram sun kaddamar da farmaki a birnin, inda ake shirin kafa hedikwatar yaki da kungiyar boko haram a kokarin da gwamanti ke yi na murkushe kungiyar ‘yan bindigar.

Rahotanni daga birnin sunce an yi amfani da rokoki da nakiyoyi a harin da ka kai yau Talata. Bayan haka kuma an ji harbe-harben bindigogi da karar jirgin sama na yaki.

Ranar Jumma’ar da ta gabata ne aka rantsar da shugaba Mohammadu Buhari, wanda ya maye gurbin dadadden shugaban kasa Goodluck Jonathan. Buhari ya bada sanarwar da shirinsa na maida Cibiyar yaki da yan boko haram kasar daga birnin tarayya Abuja zuwa garin na Maiduguri, garin da yake zaman tunga ga ‘yan boko haram.

Farmakin da ‘yan boko haram suka kai yau Talata shine na biyar tun bayan da shugaba Buhari ya hau karagar mulki.

Shaidun gani da ido sunce biyo bayan harin da aka kai ranar Asabar, wasu ‘yan kungiyar matasa, ‘yan banga sun dunguma kan tituna don hana mayakan na boko haram dannawa zuwa garin.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG