Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Amfani Da Kudi Na Yin Tasiri a Zaben Najeriya?


Yadda aka rarraba kayan aikin zabe a Kano
Yadda aka rarraba kayan aikin zabe a Kano

Yayin da ya rage kasa da shekara guda a gudanar da babban zabe a Najeriya, masana kimiyyar siyasa da harkokin dimokaradiyya da ‘yan siyasa a kasar na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da yawaitar amfani da kudi da ‘yan siyasar Najeriyar kan yi, musamman a yayin zabuka.

Masana da masu rajin wanzar da dimokaradiyya sun dade suna fadin cewa, amfani da kudi fiye da kima na daya daga cikin manyan kalubalen da demokaradiyyar Najeriya ke fuskanta.

Sai dai wannan akida ta jan hakalin masu zabe da kudi ta fi kamari ne a duk lokacin da zabe ya kusantowa a kasar.

Malam Abbati Bako, wanda ya nazarci kimiyyar siyasa da harkokin dimokaradiyya a Jami’ar Kent ta kasar Burtaniya, ya fayyace alakar kudi da salon mulkin dimokaradiyya.

Bako ya ce kudi yana daya daga cikin ka’idoji guda 57 na yadda ake yin dimokaradiyya a duniya. Haka kuma tsarin mulki ya kayyade yawan kudaden da ‘yan takara ya kamata su kashe a lokacin yakin neman zabensu.

Amma sakataren Jam’iyyar APC a jihar Kano, Hon Ibrahim Zakari Sarina, ya ce tsarin nan na "wakilai" ko "delegates" domin zaben fitar da dan takara a Jam’iyya na taka rawa wajen kwadaitar da ‘yan siyasa su wuce gona da iri game da kashe kudade a lokutan zabe.

Shi kuwa mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP mai kula da shiyyar Kano ta tsakiya Alhaji Shehu Na-Allah Kura, cewa ya yi koda yake siyasa ba ta gudana sai da kudi, amma al’umma na tursasa ‘yan siyasar wajen abin da ake kira kashe kudi fiye da kima a lokutan zabe.

Wata kididdiga da masu bibiyar kudaden da jam’iyyu ke kashewa a fagen zabe suka gudanar, ta nuna ‘yan siyasa da Jam’iyyu sun kasashe fiye da Naira Tiriliyon guda a kakar zabe ta 2015.

Domin jin karin bayani kan ko kudade na tasiri a lokutan zaben Najeriya, saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG