Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadin Gwiwa Tsakanin Dukkan Gwamnatoci Da Al'umma Shi Ne Mafita Ga Matsalar Tsaro A Najeriya


Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar

Mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya ce mayarwa sarakunan gargajiya wadansu ikon su na da daya daga inda za’a sami nasara a yaki da matsalolin tsaro.

A yayin da wasu masana tsaro ke matsin lamba ga gwamnati Najeriya a kan ta dauki yaki da matsalolin tsaro musamman a arewacin kasar da muhimmanci, masu ruwa da tsaki da suka hada da Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Gwamnonin Arewa Maso Yamma, kama daga Dauda Lawal na jihar Zamfara, Dikko Radda na Jihar Katsina, Uba Sani na jihar Kaduna, Bala Muhammad na jihar Bauchi dake Arewa Maso Gabashin Najeriya, sarakunan gargajiya da dai sauransu, sun lashi takobin kawo karshen matsalolin tsaro a arewacin Najeriya da ma kasar baki daya ta hanyar al’umma tare da cewa hada gwiwa daga bangaren tarayya zuwa jiha shi ne mafita.

Gwamna Bello Matawalle (Facebook/Bello Matawalle)
Gwamna Bello Matawalle (Facebook/Bello Matawalle)

Da ya ke bayani a taron, Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya jaddada muhimmancin hada gwiwa wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Alkawura daga bakin wadannan masu ruwa da tsakin dai na zuwa ne jim kadan bayan bude taron yini biyu na nazari a kan matsalolin tsaro da zimmar kawo mafita mai dorewa da Gamayyar Kungiyoyin Arewa wato Coalition of Northern Groups (CNG) da ta fara a yau Laraba, inda aka tafka muhawara mai karfi a kan sakamakon binciken kungiyar ta CNG don warware matsalolin wadanda suka kara kamari a makonnin baya-bayan nan.

Alhaji Nastura Ashir Shariff shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar CNG wadda ya bayyana cewa a kungiyance, sun fitar da wata manhaja da zata kula da yadda za’a yi amfani da gudunmuwar al’umma gabadaya don kawo karshen matsalolin tare da taimakawa al’ummar da matsalolin tsaro ta kassara su.

A wani bangare kuwa gwamna Dikko Radda na jihar Katsina, wanda shi ya fara kafa wata rundunar tsaro na musamman don taimakawa asalin rundunonin tsaron Najeriya yace, hadin gwiwar da ake gani tsakanin gwamnonin arewa maso yamma abu ne mai karfafa gwiwa a yaki da matsalar tsaro.

Dauda Lawal
Dauda Lawal

Shi ma takwararsa na jihar Zamfara, Dauda Lawal, cewa ya yi tattaunawa tsakanin gwamnonin arewa maso yamma da sauran masu ruwa da tsaki da kuma fitar da siyasa wajen yakar lamarin su ne kashin baya ga murkushe matsalolin tsaro a arewacin Najeriya.

Sanata Uba Sani da shi ne gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana cewa, ba wata jiha daya da zata iya magance matsalolin tsaro ita kadai, sai an hada gwiwa baya ga cewa an duba yadda za’a kawo karshen matsaloli masu alaka da tattalin arziki.

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

hakazalika, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi wanda a cewarsa ba za’a kawo gyara a matsalolin tsaro ba ba tare da gwamnoni ba kuma rashin sanya idanu daga bangaren gwamnonin ma na kara yin tarnaki ga samun nasara a kan matsalolin.

Ya ka ra da cewa sa ido akan komai a gwamnatance shi ne babban dabara.

Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bukaci dukkan masu fada a ji a arewa da ma Najeriya baki daya su guji barin bambancin siyasa ya zama matsala wurin hada kai domin a magance matsalolin tsaro.

Haka kuma, Mai Martaba, Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya ce mayarwa sarakunan gargajiya wadansu ikonsu na daya daga inda za’a sami nasara a yaki da matsalolin tsaro.

A bangare guda kuma Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce matsalar da aka samu ba’a dauki mataki da wuri a kan matsalolin tsaro ba yana mai cewa dukkan bangarorin tsaro a kasar zasu hada gwiwa wajen magance matsalolin kuma suna bukatar gudunmuwar al’umma wajen samun nasara

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Abdulsalam Abubakar, ya yi fatan cewa a karshen taron na CNG, za’a sami shawarwari ga gwamnatin kan aiwatar da mafita ga matsalolin tsaron Najeriya.

A maganar yaki da ‘yan ta’adda masu sace-sacen mutane don neman kudin fansa, masana tsaro dai na kara jaddada muhimmancin a yi amfani da bayanan banki da na lambar shedar zama dan kasa na NIN dake hade da layukan sadarwa da wasu ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen karbar kudin fansa don magance wannan matsalar.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

Hadin Gwiwa Tsakanin Dukkan Gwamnatoci Da Al'umma Shi Ne Mafita Ga Matsalar Tsaro A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG