Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sheikh Dahiru Bauchi Yayi wa Filasdinu Kyautar Naira Miliyan 100


Sheikh Shehu Dahiru Bauchi
Sheikh Shehu Dahiru Bauchi

Babban Malamin Addinin  Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ya bada gudummawar kudi Naira Miliyon dari (100) domin Taimaka wa Mutanen kasar Falasdinu da suke yaki da kasar Israila.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bada wannan gudummawa ne lokacin da aka karanta
masa wasikar da babban dan Shehu Ibrahim Nyass Khalifa Sheikh
Muhammadul Mahiy Inyass ya rubuto wa dukkan Almajiran shehu Ibrahim
cewa su taimaka a tara dala miliyan guda da ya yi alkawari cewa za’a
baiwa Falasdinawa da yaki ya tagayyara.

Babban Malamin Addinin Musuluncin kuma jagoran Darikar Tijjaniya,
Maulana Sheik Tahir Usman Bauchi. Ya shaida bada gudumawar naira
Miliyan dari daya (#1000,000 Million) wanda ya yi daidai da dalar Amurka dubu dari na kashin kansa.

Ga abinda wasikar ta kunsa daga bakin mai Magana da yawun Shehu Mahiy
a Najeriya.

Wakilin sheihin malamin ya ce, a cikin wasikar da ya rubuto, Khalifa Sheikh Muhammadu-l-Mahy Inyass, ya ari bakin almajiran shehu Ibrahin Inyass ya ci albasa inda ya yi alkawarin baiwa Falasdinu gudunmawar dalar Amurka miliyan guda sannan ko wani muridi, ko ma ba muridi ba ko dan Tijaniyya, in dai mutum Musulmi ne domin wannan batun ya shafi musulmi ne. Ya ce Shehu Ibrahim yana ta kokari da Filadinu tun yana raye, gashi kuma yanzu ana kashe su; dole mu musulmi ne zamu taimaka musu. Bayan karanta wannan wasikar, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce shi zai ba da naira miliyan dari, sannan kowa ya fadi gwargwadon nawa zai iya bayarwa a duk fadin Najeriya. Kuma duk wanda ya ce shi almajirin Sheikh maulana ne kuma almajirin shehu Tijjani ne, wannan ya zama wajibi tunda umarni ne daga khalifan mu. Amma sauran Musulmi da ba 'yan Tijjaniyya ba, bai zama musu dole ba, a cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A saurari rahoton Muhammad Abdul-Wahab:

SHEIK TAHIR USMAN BAUCHI DONATES ONE HUNDRED MILLION NAIRA TO PALESTINE.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG