Tsarin ya tanadi takardu ne, masu dauke “Makkah”, ko “Najeriya” a cikin jaka, sannan an bukaci masu sha’awar zuwa aikin hajji, su zabi takarda daya, kuma duk wanda ya dauki takarda mai dauke da “Makkah”, to zai tafi Hajji kennan. Duk kuma wanda ya dauki Najeriya, to ba zai samu daman zuwa aikin Hajji na wannan shekara ba kennan.
A shekarar da ta wuce, an yi amfani da irin wannan tsari a jihar Gombe, kamar yadda wata mai suna Aishatu ta shaida wa Muryar Amurka. A cewarta, babu adalci a cikin wannan tsari saboda alkawarin da Gwamnan jiha yayi musu a shekarar da ta wuce, a lokacin da ta kasance daya daga cikin wadanda basu samu daman tafiya aikin Hajji ba, na cewa wannan karan, zasu samu. A wannan shekara ma, bata dauko takarda mai dauke da “Makkah” a jiki ba.
Kafin hukumar ta fara tantace maniyata ta wannan tsari na “canki-canka”, sai tayi amfani da wasu sharruda tukunna. Dole sai maniyacci yana da ilimi, lafiya da kuma idan bai taba zuwa aikin Hajji ba. Masu kokawar, sun bayanna cewa fito da tsarin canki-canka din ba dai-dai bane bayan sharrudan da aka riga aka gindaya a baya.
Shugaban kwamitin tantance maniyatan, Malam Salisu Muhammad Gombe, yace wannan tsari ne na addini, kuma hukumar addini ce, bugu da kari, kuri’a halal ne a addinance balle ma idan mutane sun amince da gudanar da ita.
Ana sa ran alhazai 2,500 ne zasu samu damar zuwa aikin Hajji a wannan shekara daga jihar Gombe.
Wakilinmu, Abdulwahab Muhammed daga jihar Bauci ya tattauna da wadanda wannan tsari ya shafa.