WASHINGTON, D. C. - Paul Whelan mai shekaru hamsin da uku an haife shi ne a Canada amma kuma a yau yana da takardun shaidar dan ƙasar Amurka, Burtaniya, Ireland , da kuma Canada. Ya yi aiki a matsayin magatakardar gudanarwa a cikin Rundunar mayakan ruwa ta Amurka na tsawon shekaru biyar. Ya kuma koma rayuwar farar hula a cikin shekarar 2008, Whelan ya yi aiki a matsayin darektan tsaro na duniya da bincike na masana'antar kera motoci na duniya da ke jihar Michigan. Tun daga kusan 2006, ya fara kai ziyara Rasha akai-akai kuma ya ci gaba da kasancewa a wani shafin yanar gizon kafofin sada zumunta na harshen Rasha.
A cikin watan Disamba 2018, Whelan ya isa Moscow don halartar bikin auren abokinsa, wanda shima tsohon mayakin ruwa ne. Jami’an Hukumar Tsaro ta Tarayya ta Rasha suka kama shi a ranar 28 ga watan na Disamba, inda aka tuhume shi da laifin leken asiri, zargin da danginsa da gwamnatin Amurka suka dage ba shi da tushe balle makama. A kuma ranar 20 ga Yuli, 2020, fiye da shekara guda da rabi bayan kama shi, aka yanke wa Paul Whelan hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari. Yanzu haka yana tsare a wani gidan yari mai tsatsauran tsaro a tsakiyar kasar Rasha.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce " ranar 28 ga watan Disamba aka cika shekaru biyar tun bayan da hukumomin Rasha suka tsare Paul Whelan ‘dan kasar Amurka bisa kuskure.” “Bayan wata shari’a a boye ta bayan fage, Paul ya shafe shekaru yana aikin leburanci a wani yankin Rasha da ke karkashin mulkin mallaka. A cikin shekarar da ta gabata kadai, ya fuskanci cin zarafi daga wasu fursunoni da kuma cin zarafi daga kafofin yada labaran gwamnatin Rasha.
Sakatare Blinken ya ce " Paul da danginsa sun dade suna shan wahala sakamakon matakin da gwamnatin Rasha ta dauka na tsare 'yan kasar Amurka bisa kuskure." "Amfani da mutane a matsayin tarkon siyasa ba abin yarda ba ne. Tun lokacin da Shugaba Biden ya hau kan karagar mulki, Amurka ta samu nasara akan sakin fursunonin fiye da arba'in da ba su dace a daure ba, kuma babu wata rana da za ta wuce ba tare da gwamnatin Amurka ta yi yunkuri na dawo da Paul gida ba. Ba za mu huta ba har sai ya dawo lafiya cikin iyalansa inda ya dace.”
Wannan sharhi ne na ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna