Wannan harin kisan killar har yanzu bai fita daga zukatan mutanen da abun ya fi shafa ba.
Daliban suna barci ne cikin tsakar dare yayin da 'yan Boko Haram suka farmasu suka cinnawa dakuna kwanasu wuta. Wadanda suka yi kokarin gudu 'yan Boko Haram sun cafkesu sun jefasu cikin wuta. Wasu kuma yankasu suka yi tamkar raguna kafin su jefa gawarwakinsu cikin wuta. Yau shekara daya kenan da aukuwar lamarin.
Kungiyar "Bring Back Our Girls" masu fafitikar ganin an ceto 'yan matan Chibok 219 da har yanzu suna hannun 'yan Boko Haram sun yi zaman makoki na musamman a Abuja domin tunawa da daliban Buni Yadi.
Fatima Audu Kaka jigo a kungiyar tace suna son gwamnati ta farka. Su aiwatar da aikin da kundun tsarin mulki ya dora kansu. Tace shekara daya kenan da aka rasa daliban. Abun takaici gwamnatin tarayya ko fara bata aika ba a yiwa iyayen yaran ta'aziya. Har yau babu wanda ya gaya masu komi. Wasu iyayen suna da wasu 'yayan da suka kubuta daga makarantar. Su suka sake neman masu makarantu inda aka ce su biya kudi mai yawa amma gwamnati bata ce uffan ba.
A kungiyance zasu rubutawa ma'aikatar ilimi ta tarayya akan daliban da halin da iyayensu suke ciki.
Ga karin bayani a rahoton Medina Dauda.