Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA, ta tabbatar da adadin wadanda su ka rasu sannan akwai wasu mutane 14 da su ka samu raunuka su ke zaman jinya a asibiti.
A cewar wani ganau da ke wurin a lokacin da boma-boman suka tashi, bom na farko ya tashi a kusa da rumfar mai shayi da ke tashar motar Bauci, yayin da na biyu ya tashi a tashar motar Bauci da Gombe da ke kofar jami’ar Jos.
Sarki na Duala wanda ya ga abun da ya faru, cewa ya yi “abun da ya ke faruwa, akwai wani shagon mai shayi da ake cewa Murtala, a jikin katangar tasha. A nan bom na farko ya tashi. Na biyu kuma ya tashi a wajen tashar Bauci da Gombe, to amma wanda yafi muni shine na wajen mai shayin nan don mutane sun cika a wurin a lokacin da bom din ya tashi.”
A kwanakin baya an samu karin tashe-tashen boma-bomai a birane da dama a arewacin Najeriya, lamarin da ke saka shakku a zukatan jama’a a dai-dai wannan lokaci da aka tunkari babban zaben 2015 a watan Maris.