Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake a Biu Ya Kashe 20


Wadansu rahotanni daga karamar Hukumar Biu a kudancin Jihar Borno na nuni da cewa kimanin mutane 20 ne su ka rasa rayukan su, sakamakon harin kunar bakin wake da wani ya kai.

Alhamis dinnan, da misalin karfe 3 na rana ne dan harin kunar bakin waken ya abkawa tashar Gandu daf da shiga cikin garin Biu, inda ake dibar fasenjoji da ke zuwa kauyukan da ke kusa da garin Biu.

Wannan shine karo na uku da aka samu tashin bom a cikin makonni biyu a garin na Biu, daya daga cikin manyan garuruwan da ke kudancin Jihar Borno.

Laraban nan da ta gabata ne, wani bom shima ya tashi a dai-dai inda ake binciken ababen hawa, wanda ya hallaka mutane 17.

Sai dai bayanan da Sashen Hausa na Muryar Amurka yake samu daga garin Biu, na nuni da cewa harin Alhamis dinnan wasu mutane biyu ne suka kai shi.

Wannan tashin bom din ya zo ne a dai-dai lokacin da hukumomin tsaron Najeriya da na kasashen makwabta su ke ci gaba da fafatawa a wasu kauyuka da garurwa da mayakan Boko Haram su ka yi ka-ka-gida.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG