Manajan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Jose Mourinho na yawan amfani da kafofin yada labarai wajen kare ‘yan wasan sa daga suka, wannan dabara ce da yake yawan amfani da ita wajen karkatar da duk wata suka da akeyiwa wani ‘dan wasa zuwa kansa ko wani dabam.
Ta haka ne ake ganin cewa ya hada kan ‘yan kungiyar sa, da kada su yarda da wasu maganganu na waje, su kuma amince da junansu.
Ana haka ne dai kwatsam sai gashi Jose Mourinho ya juya kan ‘daya daga cikin tawagarsa, lokacin da ya nuna yatsa kan likitan kungiyar Eva Carneiro.
Bayan samun jan kati ga ‘daya daga cikin ‘yan wasan Chelsea Thibaut Courtois, wanda hakan ya bar Chelsea da ‘yan wasa goma cikin fili, ana haka ne Eden Hazard yaji ciwo har ta kai ga fitar da ‘dan wasan domin ya huta, wanda hakan yabar Chelsea da ‘yan wasa 9 a cikin fili.
Alokacin da Jose Mourinho yake magana da manema labarai bayan gama wasa ne yake cewa, “idan kaje duba ‘dan wasa, to dole ka tabbatar da lafiyar sa, nayi imanin cewa Eden bashi da wata matsala, an taba shi ya fadi kuma yana gajiye.
Amma masu kula da lafiyar ‘yan wasan kungiyar sun bar mu cikin yanayin karancin ‘yan wasa, wanda hakan ya saka mu cikin halin damuwa.