Matakin da masu kare hakkin dan adam suka yaba da shi. Sai dai sun gargadin mambobin kwamitin su dauki shawarwarin jama’a da mahimmanci.
Tangardar dake tattare da tsarin shara’a da dukkan abubuwan da suka jibanci hanyoyin hukunta mutanen da ake zargi da aikata laifika wata matsala ce dake cinyewa jama’ar Nijer tuwo a kwarya. Mafari kenan gwmnatin kasar ta kafa wannan kwamiti domin zakulo kura kuran dake tattare da kundayen da aka shafe shekaru sama da 60 ana aiki da su a kotuna.
Mai shara’a Maman Sani Ousseini Djibadje shine jagoran wannan tafiya. Ya kuma ce takardu ne wanda aka yi gado daga mulkin mallaka, sauran kasashe da aka musu mulkin sun dade da canza dokokin su, suka maida su dai-dai da na yanzu.
Nijar tana nata gyaran amma kadan kadan ne, yanzu ne gwamantati za ta yi gyara gaba daya. Duk wani abun da ke kawo cikas ko ba dai-dai ba, za a gyara su.
Raunin tsarin shara’a wani abu ne da ke bayyane a fili a Nijer ta la’akari da yanayin da abin ya jefa wasu dubban ‘yan kasar ciki.
Tun ba yau ba, jami’an kare hakkin dan adam irinsu Abdou Elhaji Idi na kungiyar FSCN ke jan hankula akan maganar aiwatar da sauye sauye a harkokin shara’a saboda haka su ka yi na’am da yunkurin da aka sa a gaba amma kuma shigarda shawarwarin jama’a a sauye sauyen da za a aiwatar ya zama wajibi ga wadanda aka dorawa nauyin wannan aiki inji su.
Kwamitin wanda ke kunshe da alkalan shara’a da masanan doka da jami’an fafitika da ‘yan jarida ya bude layin waya mai lamba 115 domin bai wa ‘yan kasa damar kira su bada shawarwarin da a karshe za a gabatar da su ga gwamnati.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: