Hukumomin Saudiyya sun ce a ranar Alhamis mai zuwa za a tashi da azumiNn watan Ramadana, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Da yammacin yau Talata kotun kolin kasar ta ce kalandar watan Sha’aban zai kare ne a ranar Laraba, wanda hakan ke nufin sai ranar Alhamis watan na azumi zai kama.
Da safiyar yau ne hukumomin kasar suka umurci ‘yan kasar da su fara duban jinjirin wata, wanda shi ne zai yi nuni da shigar watan na Ramadana, amma kuma ba a gan shi ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ta Saudiyya ya ce.
Kazalika a kasar Qatar da ke makwabtaka da Saudiyyar, kwamitin duban wata ya sanar da cewa Alhamis ce ranar farkon watan na Ramadana.