Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Mutane a Jahar Ekiti


Satar Mutane
Satar Mutane

Satar Mutane a jahar Ekiti ta zama ruwan dare gama duniya, harma wani lauya mai fafutukar 'yancin dan adam ya ce laifin gwamnan jahar ne.

Cigaba da sace mutane da yin garkuwa da su na cigaba da tada hankalin jama'a a jahar Ekiti harma ya kaiga zargin gwamnan jahar da nuna halin ko oho akan lamarin duk kuwa alkawuran da aka yi na kawo karshen matsalar, a kwana kwanan nan an sace mutane goma cikin makwanni biyu.

A rahoton da Babangida Jibril ya aiko wa da sashin hausa na nuna cewar a karshen makon da ya gabata dai an sace mata uku da mazajen su da kuma yara, amma masu garkuwa da su sun sako mazaje uku da kuma kananan yaran amma har yanzu babu duriyar inda matan suke.

Yanzu haka akwai tsohon shugaban asibitin koyarwa na jami'ar Ekiti da matar sa da kuma wata malamar jiyya da malamin jami'ar Obafemi Awolowo da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutanen kuma har yanzu babu duriyar su.

Jama'a sun fara dora laifin sace sacen mutanen akan gwamnan jahar wanda ke fuskantar tsigewa daga 'yan majalisar jahar na jam'iyar APC.

A wata sanarwar da ya rabawa manema labarai, wani lauya mai fafutukar kare 'yancin dan adam ya fitar a birnin Lagos Mr Femi Falana, ya zargi gwamnan da gazawa. kuma yace gwamnan ne ke daure wa 'yan bindiga da masu satar jama'a gindi a jahar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG