Sha'anin tabarbarewar tsaro shi ne ya dauki hankalin jama'a domin yadda aka tsananta matakan tsaro a duk fadin birnin Sokoto, tuni ne ga kowa cewa kasar tana cikin wani mawuyacin hali. A cikin jawabinsa ga duk al'ummar Musulmin Najeriya Maimartaba Sarkin Musulmi Mohammad Sa'ad Abubakar ya mayarda hankalinsa bisa ga halin da arewa da ma kasar gaba daya ke ciki. Ya ce yanayin kasar yanzu ya kai lahaula kuma wajibi ne gwamnati ta kara kokari bisa ga wanda ta keyi yanzu domin kawo karshen zubar da jini da salwantar da dukiyoyin jama'a. Maimartaba ya ce maganar tsaro muhimmiya ce a wurinsa kuma duk abun da zai kawo zaman lafiya suna na'am da shi.
Maimartaba ya yi mamakin yadda wasu ke sukan kwamitin sulhun da gwamnati ta kafa duk da cewa kwamitin ya shukar turbar kawo gyara. Ya ce wadanda suke cewa a rusa kwamitin marasa kishin kasa ne kuma marasa son zaman lafiya. Ya ce kamata yayi a goyi bayan kwamitin domin aikin da yake yi. Ya ce su suna na'am da aikin kwamitin kuma zasu cigaba da bashi hadin kai domin ya samu nasarar aikinsa.
Sarki Sa'ad ya kira malaman addini na Musulmai da Krista su ji tsoron Allah su rika koyas da abubuwan da zasu kawo zaman lafiya da hadin kai. Su fadakar da mabiyansu da su kuma dena tsangwama da sukan juna ta yadda zasu kawo kiyayya da tashin hankali a kasar Najeriya
Daga karshe Sarki Sa'ad yayi amanna cewa adalci da gaskiya daga shugabanni da masu rike mukaman siyasa su ne babban jigon kawo zaman lafiya da cigaba kasar. Ya ce yawancin shugabannin abun duniya suka sa gabansu. Sun manta da hakkin al'ummominsu da Allah Ya dora masu. Su kansu shugabannin basa bin dokokin kasa ko na Ubangijin da Ya haliccemu. Ya kira shugabanni da su ji tsoron Allah akan amanar da Ya sa a hannunsu.
Murtala Faruk Sanyinna nada rahoto.