Sai dai duk da dokar tun da safe jama'ar Musulmi suka tafi masallatan hawan idi domin yin sallar kawo karshen azumin wannan shekarar. Bayan sallar jama'a sun yi ma juna murna da yin nishadi. Haka kuma mutanen gari da manyan gwamnati sai suka nufi fadar Lamidon Adamawa su yi gaisuwar salla kamar yadda aka saba yi. Lamidon Adamawa Dr. Barkindo ya mika gaisuwarsa ta salla ga jama'a. Ya taya musulmai murna inda ya yi fatan Allah ya sa albarka bisa ga aikin ibadan da suka kammala ya kuma sa aga badi lafiya. Ya gargadi al'umma su nemi zaman lafiya da hadin kai.
A jihar Taraba bikin an yishi cikin tsanaki kamar yadda wani mazaunin garin Donga Alhaji Yahudu Donga ya shaida. Ya ce bayan an ci abinci sai abi dangi ana gaisawa ana zumunci domin haka shariar Musulunci ta tanada. Idan kuma akwai wani da kuke gaba da shi sai a yi kokari a nemi gafarar juna. Rana ce ta farin ciki ta kuma yafewa juna.
Tun daga bisani gwamnatin tarayya ta tsayar da ranakun Alhamis da Juma'a domin hutun sallah. A wani halin kuma shugaban kasar Najeriya da gwamnoni sun yi fatan Allah ya ba kasar ta Najeriya zaman lafiya da kawo karshen tashin tashina dake yawan kaiga rasa rayuka.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.