Bayan sun kammala taron ne Muryar Amurka ta tuntubi kwamishanan 'yansandan jihar Bauchi Garba Baba Umar domin karin haske.
Injishi, Garba Baba Umar yace wasu mutane ne da suka kai wajen dubu daya suka shigo cikin Bauchi akan babura dari biyar. Wai mutanen suna zuwa gida gida suna kama mutane suna kashesu.
Kwamishanan yace dalilin gayyato shugabannin Fulani ke nan domin su bayyana wa 'yansandan ko su wanene mutanen. Tambaya ta biyu shi ne abun da yakamata a yi domin a samu zaman lafiya a jihar, musamman tsakanin Fulanin da Manoma.
A Bauchin akwai zargin cewa bayan an kama mutum da wani laifi cikin 'yan kwanaki kadan sai 'yansandan su saki mutumin.
Kwamishanan 'yansanda yace su aikinsu shi ne suyi bincike. Idan sun sami mutum da laifi saisu kaishi kotu. Yace ba su ne suke shari'a ba. Akan wannan batun kwamishanan yace ya je ma'aikatar shari'a inda ya kai karafinsa akan abun dake faruwa.
Yace wadanda ake anfani dasu suna fitar da mutanen da ake zarginsu da laifinkisa ko satar mutane da dai sauransu suna cikin 'yansanda da ma'aikatar shari'a da sarakuna da wasu manyan gari dake rike da mukamai su ne suke sa ake sakin masu aikata laifi. Yace duka irin wadannan zasu yi maganinsu.
Alhaji Ahmed sakataren kungiyar Miyetti Allah reshen jihar na cikin wadanda suka halarci taron. Yace sun lura sha'anin tsaro ya tabarbare kuma bisa ga wasu dalilai akwai 'yan kungiyarsu a ciki. Yace sun dade suna yaki akan yadda za'a rage tabarbarewar tsaron ta fahimtar da mutanensu. Yace da kwamishanan 'yansandan ya kira taron suka kasance a wurin domin su bada tasu gudummawar.
A kan zargin da ake yiwa Fulani cewa suna aikata ba daidai ba yace a kowace kabila ko kungiya akwai bata gari. Amma babu wata kungiyar da zata ce ita tana cikin masu tada zaune tsaye. Yace su suna biyayya da jami'an tsaro kuma masu tada hankali su basu sansu ba.
Sarkin Fulanin garin Buzayi Alhaji Muhammad Useni shugaban Fulanin Kautar Hore ya halarci taron yace yaya za'a yi a ce mutum ya shigo gari ba'a sani ba. Ya kamata a fitar da duk abun dake cikin duhu fili. Yamakata shugabannin al'umma su tantance kowane bako kafin a saukeshi.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Facebook Forum