Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta gabatar wa manema labarai wasu gungun masu fashi da makami da take zargi da yin fashi da makamai a wani banki dake garin Offa inda aka kashe mutane fiye da 30 da suka hada da ‘yan sanda.
‘Yan fashin sun yi zargin cewa su yaran gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki ne. Sun ce wadan nan shugabanin ne suka basu kayan aiki da makamai.
To sai dai gwamnatin jihar ta Kwara ta fito ta musanta zargin. Ta ce bata da muamala ko cudanya da masu fashi da makamin. Dr. Muidin Akorode mataimakin gwamnan jihar na musamman akan labarai ya ce gwamnan jihar ko wani na kusa dashi bashi da wata muamala da ‘yan fashin, walau ko ta kudi ko kuma ta wata hanya daban. Saboda haka gwamnan ya yi watsi da zargin na ‘yan sanda.
Dr. Akorede y ace ko shakka babu shi ma shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki zai fito fili ya yi watsi da zargin na ‘yan sanda.
A saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.
Facebook Forum