Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Sanders Zai Gana da Hillary Clinton Wannan Makon


Hillary Clinton wadda ta lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat
Hillary Clinton wadda ta lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat Senata Bernie Sanders, mai wakiltar jihar Vermont, yace a shirye yake ya gana da wacce ta sami nasarar zama 'yar takarar shugabancin kasa Madam Hillary Clinton, bayan da aka yi zabe na karshe Talata mai zuwa a nan Washington. Zasu tattauna kan ajendarsu kamin ya yanke shawara ko zai dakatar da yakin neman zaben da yake yi.

Sanders wanda yayi magana jiya Lahadi cikin shirin tashar talabijin ta NBC da ake kiraMeet the Press, yace babban burinsa shine kada hamshakin attajirin nan da jam'iyyar Repubican ta tsayar watau Donald Trump ya zama shugaban kasa.

Duk da haka yace da farko yana son ya tabbatar da cewa Mrs Clinton tana goyon bayan ajendarsa na yaki da tasirin da masu hali suke da shi ta fuskar siyasa, da kuma batun gibi dake akwai tsakanin masu hali da marasa galihu a Amurka, kamin ya yanke shawara kan irin goyon bayan da zai bata.

Magoya bayan Mr Sanders suna da ta cewa wajen tsara alkibla da manufofin jam'iyyar a lokacin babban taron jam'iyyar da za'a yi watan gobe a Philadelphia. Sanders ya kada Hillary a jihohi 22, kodshike ita kuma ta yi nasara a jihohi 28, kuma tana gaba da shi da kuri'u fiyeda milyan uku da dubu dari bakwai.

Amma Trump yana fuskantar rarrabuwar kawuna a jam'iyyar Republican fiyeda abunda Mrs Clinton take fama da shi. Shugabannin jam'iyyar suna kwabar Trump saboda sukar da yake yiwa wani alkali wanda yake sauraron karar da aka shigar kan tsohuwar jam'iar Trump.

Tsohon dan takarar shugabancin jam'iyyar Mitt Romney, yace abunda Trump yayi bashi da wani suna illa nuna banabancin launin fata ko harshe.

BERNIE SANDERS
BERNIE SANDERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG