Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana'a Maganin Samari Masu Yaudara - Inji Khadija


Khadija Abdullahi
Khadija Abdullahi

Khadija Abdullahi buduwa ce wacce ta kammala makarantar sakandire kuma bata samu damar cigaba da karatunta na gaba da sakandire ba sakamakon rashin karfi na tattalin arziki da iyayenta ke fama da shi, sakamakon hakanne ta fara sana’a.

Khadija ta ce tana sana’ar sayar da takalma da sarkoki irin na kasar India , ta hanyar tallata hajarta a kafar sadarwa ta Whatsapp domin 'yan uwa da abokan arzika su ga kalar kayan domin su bayyana sha’awarsu ko kuma su saya.

Khadija ta kara da cewa babban abinda ya sanya ta fara wannan sana’a bai wuce yadda ta lura da cewa mafi yawan samari da zarar budurwa ta fara tambayarsu wasu 'yan kudade sai su fara neman wani abu a wajen ta a madadin kudin da zasu baiwa mace, a cewarta hakan na daya daga cikjin dalilan da suka sa ta fara sana’a

Khadija ta kara da cewa kamar sauran kananan sana’o'i, ita ma ta fara fuskantar matsaloli na bashi inda wasu da zarar sun karbi kayan ka sai ka yi da gaske kafin su biya bashin da ake binsu.

daga karshe ta kara da cewa babban burinta dai ta zama babbar 'yar kasuwa da za’a rika sarar kaya a wajenta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG