Dr Fatima Muhammed, kwararriyar ma’aikaciyar lafiya wadda ta kammala karatun ta a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, jihar Kadu ta bayyana irin gwagwarmayar data sha musamman a lokacin da take karatu a jami’a.
Daya daga cikin kalubalen da yawancin dalibai ke fuskanta shine barin gida, iyaye da sauran dangi domin zuwa wani wuri ko kasa neman ilimi, tabbas haka lamarin ya kasance ga matashiyar, domin kuwa a cewar ta baya ga tarin karatun litattafai data tsinci kanta a ciki ta kasance cikin kewar gida.
Dr Fatima ta ci gaba da bayyana cewa “ina kammala karatun gaba da sakandire na sami gurbin karatun likitanci a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ban sami wani jinkiri ko matsala ba”.
Kamar yadda aka tsara, duk dalibin da ya yi karatun aikin lafiya wato likitanci, makaranta kan tura shi yin wani dan gajeren zango na fara aiki a mataki na gaba wanda ake kira House Manship, Dr Fatima ta kammala nata ne a jami’ar Bayero dake jihar Kano.
Bayan ta kai nataki na karshe, ta yi aikin yiwa kasa hidima duk a jihar Kano, kuma daga karshe ta bayyana jin dadin ta musamman yadda bata taba samun matsala da abokan aiki ba, duba da yadda yawancin likitoci ke samun kawunan su ciki.
Daga karshe ta yi kira ga mata da su nemi ilimi domin kuwa a cewar ta alfanun sa ya fi gaban a musalta, domin kuwa ko badan aikin gwamnati ba, ilimin 'ya mace amfani gare musamman ga 'ya'yan ta, zaman aure da sauran su.
Facebook Forum