Kotunan dake bin bahasin zabubbuka na Najeriya a bana, sun soke zabubbuka da dama, kamar na gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers tare da kakakin majalisar dokokin jihar, da kuma na sanatoci a jihohi kamar Taraba da Ogun.
Wani lauyan da ya kware kan tsarin mulkin kasa, Barrister Mainasara Kogo Ibrahim, yace karuwar kararraklin da ake shigarwa da kuma karuwar dokokin da ake yin aiki da su a kasa, sun taka rawa. Yace a shari'ance, ganin wani irin hukumci da kotu ta yanke, zai iya sanya wani ma ya shigar da kara idan batunsa yayi kama da wancan bisa sa ran cewa shi ma zai samu irin wannan biyan bukata.
Wani dan siyasa matashi, Mammadu Lawal Arabi, shi korafi yayi kan yadda ake gudanar da shari'ar zabe a jihohi dabam-dabam. Yace an samu yanayin da aka yanke hukumce-hukumce kishiyoyin juna a kan kararrakin da suka yi kama sosai a jihohi dabam-dabam.
Ya kara da misalin yadda hukumar yaki da zarmiya da cin hanci ta EFCC take kama mutane da laifin satar dukiya, amma sai kotuna su rika sake su.
Ga cikakken rahoton Hassan Maina Kaina