Ganin yadda Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ta dage wajen kama wasu tsoffin gwamnonin jahohin Najeriya da su ka cuci jama’a, masu fashin baki na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu. Cikin tsoffin gwamnonin da aka damke a baya-bayan nan kuma su ke cigaba da bayani ga hukumar ta EFCC, har da na Benue, Kebbi da Akwo-Ibom.
Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum mai suna Kanti Alhaji Uba Na Alhaji Barau ya ce akasari gwamnoni su kan mance cewa za a tambayesu su yi ta barna yayin da su ke mulki saboda su na da kariya a lokacin. Y ace don haka ne ma su kan yi dauki dora saboda masu goyon bayansu su gaje su kar asirinsu ya tonu. Y ace dayake yanzu ana kwatanta adalci, duk wanda ya yi barna ana bin diddigi. Ya ce akasari ma idan EFCC ta kai mutum kotu sai magana ta shiririce. Wannan, in ji shi, shi ke sawa na baya su kasa wa’azantuwa.
Shi kuwa kwamrad Abubakar Abdulsalam, jagorar wata kungiyar rajin yaki da cin hanci da rashawa ya yi nuni da yadda kwanakin baya wasu tsoffin Shugabannin Najeriya da wasu shugabannin addinai su ka ziyarci Shuagba Muhammadu Buhari su ka roki da ya sassauta matakan da ya ke daukawa kan cin hanci da rashawa. Ya ce haka ba ya taimakawa. Amma da aka fara daukar matakai gadan-gadan kan masu satar dukiyar jama’a, kowa ya fara shiga taitayinsa in ji shi.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton: