Mafi yawancin jama’ar da aka baiwa horo ‘yan Najeriya ne wadanda tarzomar Boko Haram ta raba da gidajensu.
“Sunana Junaidu Jibrin Maiba, mun amfana mun karu sosai zaman mu a wannan waje, musammam wajen tabbatar da tarbiyya, da bamu hanyoyi da zamu zama mutanen kan mu, wajen cigaban kan mu gaba daya.”
It kuwa Omelikan Daniel daga Jihar Adamawa cewa ta yi “mun koyi cewa sai an hada kai. In ba’a hada kai ba an yi shawara an yadda da juna, baza a iya tsallaka ruwa ba.”
“Sunana Usman Bukar daga Jihar Yobe. Mun koyi yadda zamu zama shugabanni na gari. Hakikanin gaskiya babu yadda za’a yi mutum ya zama shugaba na gari sai ya so wa dan uwanshi abunda yake so wa kan sa. “
Daya daga cikin jami’an da suka horas da matasan yayi wa Sashen Hausa na Muryar karin haske akan irin horaswa da suka baiwa matasan. Adamu Maimako malami ne.
“Zamu koya musu zaman lafiya, akwai kuma sana’o’i da yawa wanda aka koya musu a cikin sati biyu.”