Kerry ya soke ziyarar bayanda shugaba Abbas yace hukumomin Falasdinu ba tareda wani bata lokci ba zasu ci gaba da daukan matakai na neman yardar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a matsayin kasa, har tuni yankin ya tura bukatar neman zama wakili a hukumomin MDD 15.
Nan da nan dai, Isra’ila bata ce kome ba akan wannan mataki, sai dai jami’an kasar jiya talata sun sake gabatar da takardun aikin gina gidajen ‘yan share wuri zauna fiyeda dari bakwai a gabashin birnin kudus.