Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Shawarci Shuwagabannin Isra'ila Da Falasdinu


Hoton Shugaba Obama kennan a lokacin da yake ganawa da Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas.
Hoton Shugaba Obama kennan a lokacin da yake ganawa da Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas.

Shugaba Barack Obama na Amurka yayi kira akan shugabannin Isra’ila da Palesdinu da cewa su soma tattaunawar sulhu a akan matsalolin dake tsakaninsu ba tareda jira sai ranar da zasu zauna da junansu da sunan neman warware matsalolin dake gabansu ba.

WASHINGTON, D.C - A yau Alhamis ne shugaban yake bada wannan shawara a lokacinda shi da shugaban Palesdinawa Mahmud Abbas suke bayyana gaban manema labarai a Ramallah, wuri na baya-bayan nan da shugaba Obama ya yada zango a cikinsa, a ci gaban rangadin da yake kaiwa zuwa Isra’ila da Yammacin Kogin Jordan.

Shugaba Obama yace ba wani anfanin “gudanarda duk wasu shawarwari” idan aka ce daya daga cikin kasashen biyu tana jiran sai ranarda su biyun zasu zauna ido-da-ido, su warware dukkan matsalolin dake gabansu.

Shugaba Abbas ya sha nanata cewa shi ba zaiyi wata tattaunawa da isra’ila ba sai ta ja burki ga aikin da take na ginawa Yahudawa gidaje a Yammacin Kogin Jordan dake gabashin birnin Kudus, wurare biyu da Palesdinawa ke cewa nasu ne.

Frayim-ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jima yana kira akan shugaba Abbas da su zo suyi tattaunawar kai tsaye da juna.
XS
SM
MD
LG