Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sadiya Haruna Ta Sake Aure


Sadiya Haruna da ango
Sadiya Haruna da ango

Jarumar TikTok, Sayyada Sadiya Haruna ta sake amarcewa a wannan Juma'a watanni baya mutuwar aurenta da jarumin TikTok Al Ameen G-Fresh.

A wani kati da ta wallafa a shafinta na Instagram, Sadiya ta bayyana sunan angon nata a matsayin Hon. Babagana Audu Grema.

An daura auren ne da misalin karfe daya baya sallar Juma'a kamar yadda katin ya nuna a birnin Maidguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriyia.

Auren na zuwa mako guda bayan da jarumar ta TikTok ta bayyana a shirin tattaunawa na jarumar Kannywood Hadiza Gabon "Gabon Talk Show" inda Sadiya ta caccaki G-Fresh tare da bayyana matsalolin da suka kai ga mutuwar aurenta da shi.

Auren har ila yau na zuwa ne kwana guda bayan da shirin na Gabon ya watsa tattaunawar mayar da martani da G-Fresh inda shi ma ya yi ta sukar tsohuwar matar tasa - mafi aksarin lokuta a kaikaice.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG