Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sadiya Adamu Fari: Ina Da Shago Biyu Da Ma'aikata 15 A karkashina


Sadiya Adamu Fari
Sadiya Adamu Fari

Sadiya Adamu Fari matashiya mai sana’ar dogaro da kai wacce ta karanci Microbiology, a hirar su da wakiliyar DandalinVOA, ta ce ta samu Naira miliyan 10 daga shirin "You Win," tare da samun horo na musamam daga gwamnatin Najeriya, wanda da ya ba ta karfin kafa sana’ar harkar gyaran gashi da gyaran jiki, har tana da ma’aikata akalla mutum 15 a shago biyu yanzu.

Ta ce bayan kammala karatunta ne ta ji a abin da ta karanta a makaranta bai dace da ita ba tun daga farko, domin ta kasance 'yar kasuwa ce, wanda tun tana sakandare ne ta fara sayar da hajja.

Sadiya ta kara da cewa, ko bayan da ta kammala jami’ar ma, sai ta ci gaba da fara harkar gyaran gashi har ta kai da samun tallafin na gwamnatin tarayya,.

Ta ce tana da saloon na tafi da gidanka inda ake bin kwastama duk inda yake domin a yi masa aiki. Ta kara da cewa daga cikin kalubalenta shi ne sai ta koyar da ma’aikaci, kwatsam sai dare daya su daina aiki.

Wasu daga cikin ma’aikatan Sadiya kamar Ummi S. Fari ta ce ta shafe kimanin shekaru biyar tana tare da Sadiya a matsayin mai kunshi, bayan ta kammala karatunta na sakandare inda ta fara yi wa mutane kunshi, amma daga baya ta koyi yadda ake wasu ayyukan gyaran jiki.

Ummi ta ce ta koyi yadda ake kwalliya, da kuma yadda ake gyaran gashi, gyaran kafa, da ma na hannu, sannan ta koyi yadda ake mu’ammala da mutane.

Ita kuwa Aisha Muhammad wata ma’aikaciya a saloon din Sadiya, ta ce, bayan ta fara ne da shekara daya ta koma jam’ia, kuma a yanzu tana karatu a hannu guda kuma tana aikin idan ta samu dama.

Ta ce musamman ma a lokutun hutu na sallah ko duk wani hotu domin taimaka mata a shago. Ta kara da cewa zama a shagon ya koya mata yadda ake zama da mutane, da kuma zaman dogaro da kai.

A saurari cikakken hirar su da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:14:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG