Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Diyar Mallam Aminu Kano Ta Yi Bayanin Mu'amalarta Da Mahaifinta


Mallam Aminu Kano
Mallam Aminu Kano

Maryam Aminu Kano ita ce kadai da Mallam ya haifa kuma ta bayyana cewa tana da shekaru 10 da haihuwa a lokacin da Allah ya yi masa rasuwa. To ko me za ta iya tunawa dangane da mahaifinta? Sai ta sanar da mu cewa, Mallam mutum ne mai kawaici.

"Kafin ya yi min komai, sai ya fara yi wa sauran 'ya'yan 'yan uwansa," inji Maryam

Duk da cewa Allah bai ba shi haihuwa fiye da guda ba, Mallam ya rike 'ya'yan kaninsa, da na matarsa marigayiya Hajiya Shatu, kuma ya rike su tamkar na cikinsa babu banbanci.

" A lokacin ko makaranta ya sa su sai ya ba su sunansa su yi amfani da shi," inji ta

A batun tarbiyya kuma ya yi iya bakin kokarinsa wajen sa su a kan turba mai kyau.

"A lokacin idan muka kai masa kara cewa, wane yayi zagi, sai ya ce a yi sauri a kira wanda yayi zagin. Idan ya zo sai ya tambaye shi, 'Me ya sa ka yi zagi? Ka ko san zagi ba shi da kyau? To ka yi maza-maza ka je ka kurkure baki.' To tun a lokacin na gane aibin zagi, kuma na hana kaina yin sa ko yarana ba za ka taba jin zagi a bakinsu ba."

Gidan Mallam ya kasance mai cike da jama'a, da almajiransa na karatu ko na siyasa a ko da yaushe. To ko ya rayuwa ta kasancewa iyalen Mallam bayan rasuwarsa?

"Har yanzu gidanmu ba ya rubuwa da mutane, musamman talakawansa idan suna da bukata mu na taimaka musu, idan kuma ba mu da shi, sai mu ba su hakuri."

Mun nemi sanin ko almajiran Mallam, musamman wadanda suka kasance manya a kasar, su na tallafa masu kamar yadda mallam ya musu? Sai ta shaida mana cewa:

"Wadanda suka zauna tare da mallam kuma babu abinda bai yi musu ba, su ya kamata su bada wannan amsar ba ni ba. In suna yi sun sani, haka kuma in ba su yi, sun sani."

Gidan Mallam Aminu Kano
Gidan Mallam Aminu Kano

Mallam ya shahara a fannin siyasa, to ko a matsayinta na diyarsa daya tilo tana da sha'awar bin sahunsa?Ta ce na'am, sai dai siyasar ta rikide yanzu.

"Siyasar da tana da akida, ta yanzu kam gaskiya, sai a hankali - saboda ta kudi ce, idan baka da kudi, ko ka fito, ba mai kallonka. " inji Maryam

Ta yi bayanin cewa yanzu an cusa wa jama'a son kudi saboda haka siyasar ta rikide.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG