Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar PDP Ta Ce An Hana Ta Taro A Bauchi


Alamar PDP
Alamar PDP

Bangaren PDP da ya balle karkashin Alhaji Abubakar Kawu Baraje ya ce 'yansanda sun hana shi yin taronsa a otal din Awalah da ke Bauchi a karshen mako.

Sabuwar jam’iyyar PDP ta zargi ‘yan sanda da hana ta gudanar da taronta a Bauchi a karshen mako. Da ya ke yi wa wakilinmu na Bauchi Abdulwahab Muhammad bayani Shugaban Kwamitin Sabuwar PDP a jihar ta Bauchi Hon Muhammad Lawal Isah ya ce sun cika dukkannin sharuddan yin taro ciki har da rabuta wasika sa’o’i 48 kafin taron.
Ya ce har Kwamishinan ‘Yan sanda ya gayyace su tare da yin alkawarin ba su ‘yansandan da za su kare lafiyarsu.

Ya ce amma da su ka je wurin sai abin ya canza. Saboda ‘yansanda sun hanu kuma shi kan sa Kwamishinan ‘Yansanda jihar Bauchi Alhaji Mohammed Ladan ya zo ya jaddada cewa an hana taron. Wani mahalarcin taron mai suna Abubuwar Bawa Chali ya tabbatar da abin da shugaban Kwamiti din sabuwar PDP din ya ce.

To saidai da ya ke maida martani, Kwamishinan ‘Yansandan jihar Bauchi Mohammed Ladan ya ce ba gaskiya ba ne cewa da farko Rundunan ‘Yansandan jihar Bauchi ta amince sabuwar PDP din ta yi taronta. Ya kuma ce sam babu wanda ya tarwatsa masu shirin taron. Ya ce da ‘yan sabuwar PDP su ka gabatar da bukatarsu ta yin taro Rundanar ‘Yansandan ta yi nuni da kasancewar maganar a kotu. Yace Rundanar ta shawarce su da su hakura kotu ta yanke hukuncin karar da aka kai kafin a san abin yi game da taro irin wannan da su ke so su yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG