A yau dandalinVOA ya zanta da wanda ya shirya Fim din ‘Hangen nesa fim ne da ya kunshi ilimin ‘ya’ya mata, tare da nuni da muhimmancin ilimi mussamam ma ga mata tare da fito da hanyoyin koyon harshen turanci ta hanya mafi sauki inji mai shiryawa Mu’azu Harauna wanda aka fi sani da M M Haruna.
Ya ce fim din yayi duba ne kan harkar ilimi, domin koyar da harshen turanci a fannin ilimi na daya daga cikin muhimmai abubuwa da ke damun mutanen arewa mussamman ma ta fannin yin turanci a wuraren taro da sauransu.
Ya kara cewa fim din dai na nuni ne da wani gwamna da yake kunyar fito da matarsa domin bata jin harshen turanci har ta kai shi ga ya nemo wata matar wacce take jin turanci kwatsam wata rana sai ga matar tasa ladar gona ta fito bainar jama’a tana harshen turanci inda ya razana yake kuma jimamin a ina ta koyi turanci.
MM Haruna, ya kara da cewa, babban abin sha’awa a fim din shine akwai hanyoyin da za’a koyi harshen turanci cikin sauki sannan ya nuna cewar ba’a girma da neman ilimi, ya kuma taba hanyar zamantakewa da yadda mace ya kamata ta zauna da mijinta tare da nuna muhimmancin ilimin addini da na boko a lokaci guda, ganin yadda zamani ke sauyawa.
Facebook Forum