Daga watan Disambar bana gwamnatin Najeriya za ta daina shigowa da shinkafa ta tashar ruwa.
Bunkasar noma ya wadata arziki a tsakanin manya da matsakaitan manoma amma bai yi tasiri yadda ya dace a tsakanin masu awo ba.
Hakan ya sanya wasu daga cikin talakawa ci gaba da korafin rashin samun saukin rayuwa daga tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnatin APC mai mulki.
Kwamishinan kasuwanci na Sokoto Aminu Bello, ya ce gini ba ya yiwuwa a dare daya, amma in mutane su ka kara hakuri za su samu warakar kuncin da su ke ciki.
Ga bangaren fitar da kayayyakin amfanin gona ketare, shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa Barista Hassan Bello, ya ce an fara fitar da citta, da ridi daga tashar sauke kaya ta kan tudu da ke Kaduna. Bello ya ce da zarar an kammala sada tashoshin teku na kan tudu da layin dogo, lamuran kasuwancin zai kara bunkasa.
Masanin tattalin arziki kuma tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Dakta Obadiah Mailafiya, ya shawarci Shugaba Buhari ya jawo masana tattalin arziki da za su rika bitar hanyoyin ci gaban tattalin arziki a Najeriya domin samun nasara.
Dr.Mailafiya na da ra'ayin cewa koma bayan da ake samu a tattalin arzikin Najeriya, a saboda rashin ingancin tsare-tsare da kuma rashin kwararru a fadar Aso Rock. Haka zalika, Mailafiya ya ce akwai masu yi wa Shugaba Buhari zagon kasa kan lamuran tattalin arziki.
Facebook Forum