A Jamhuriyar Nijar ana tai kai ruwa rana tun bayan da hukumomin sufuri suka umurci masu ababen hawa da su musanya lasisinsu da wani sabon fitowa, tare da biyan wasu makudan kudade ga kamfanin da aka bai wa kwangilar sabon lasisin.
Dalilin wannan rikici shi ne, wasu ‘yan kasar sun nuna damuwa game da hanyoyin da aka bi wajen bayar da wannan kwangila ta dubban miliyoyin cfa.
A ranar 18 ga watan Yulin da muke ciki ne Ministan suhurin Nijar Karidjo Mamadou ya bada sanarwar bullo da wani sabon lasisin tuki da aka kira na zamani.
Saboda haka ya dibarwa masu ababen hawa wa’adin shekara 1 wato daga ranar 22 ga wata, su musanya tsohon lasisin ko kuma su huskanci hushin hukuma.
Sai dai a taron manema labaran da suka kira, kungiyoyin direbobi sun yi watsi da wannan tsari.
A yayin da darektoci ke kare manufofin Ministan suhuri, su kuwa ma’aikatan kwadago a ofishin Ministan na da tunanin da ya sha bamban, domin a cewarsu cikin yanayi mai cike da hazo aka bayar da kwangilar buga sabon lasisin kamar yadda sakataren yada labaran kungiyar SYNPAT Oumar Moussa ya bayyana.
Ana bukatar mutum ya biya 19,200 na cfa ga duk mai fatan musanya lasisinsa don samun sabon lasisin na zamani, mai wa’adin shekaru 5.
Amma a jiya Litinin an fidda sanarwa cewa farashi ya fado zuwa 14,000 na cfa, a bisa umurnin hukumomi.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum