Jami’an jihar Kaduna sun bayyanawa Kwamitin binciken lamarin a ranar Litinin din data gabata cewa, an binne mutanen ne biyo bayan hatsaniyar da mabiya Shi’ar da sojoji a garin Zaria cikin watan Disambar bara.
Shugaban reshen kungiyar Amnesty da ke Kaduna M. K. Ibrahim yace, “wannan sanarwa mai razanarwa game da bibbindige ‘yan shi’ar da tona kabarin da aka binne gawarwakinsu, shine matakin farko da ya kamata a yi domin gurfanar da duk wadanda ake zargi da aika-aiakar.
Shugaban Hukumar al’amuran addinai ta jihar Kaduna Muhammad Namadi Musa, ya fadawa Kwamitin cewa, an umarceshi da bin tawagar Kwamishinan ‘Yan Sandan Kaduna don zuwa Zari’a, inda yace yaga dimbin gawarwaki a kan titi da suka hada da mata da yara cikin bakaken kaya.
Ya kuma ce an kidaya gawa 156 a asibitin Jami’ar Ahmadu Bello aka kuma karbi wasu gawarwaki 191 daga asibitin barikin Soji na Zaria. Wani ma’aikacin lafiya a asibitin Jami’ar ta Zaria kansa yace sai da ya kidaya gawarwaki akalla 400, suma mazauna unguwar da aka yi rikicin sun ce gawarwakin da suka cika kan titin wajen na da yawa sosai.
Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai yace sun aikata abinda ya faru a Zaria ne bisa dokar da aikin Soja ya tanada. Su kuma ‘yan Shi’a sun musanta cewa sun kaiwa Hafsan Sojan hari kamar yadda ake fada.
A baya dai an zargi sojojin Najeriya da cin zarafin bil’adama akan ‘yan Boko Haram wanda sojin suka ce basu yi wani mugun abinda bai kamata ba.
Ga karin bayani.