To sai dai Jakolo ya kalubalanci cireshi da akayi a babbar kotun jihar Kebbi, wadda ta yanke hukuncin cewa an cireshi ba bisa ka’ida ba don haka tayi umarni da adawo da shi kan kujerarsa, kasancewar gwamnatin jihar a karkashin tsohon gwamna Sa’idu Dakin Gari bata daukaka kara ba. hakan yasa sarkin Gwandu mai ci ya daukaka kara a babbar kotun daukaka kara dake zamanta a Sokoto.
Kotun dai tayi watsi da karan da aka daukaka tare da tabbatar da hukuncin kotun ta jihar, bisa hujjar cewa an cire sarki Jakolo ne ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya sabawa sashe na 6 da sashe na 7 na dokar nadawa da cire sarakuna ta jihar Kebbi. Da kuma sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Bayan mayar da Jokolo kan kujerarsa kotun ta bayar da umarnin biyan shi dukkan hakkokinsa da ba’a bashi ba a matsayin sarkin Gwandu na tsawon shekaru 10 yan watanni da aka cire shi.
Domin karin bayani.