Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iheanacho Da Kungiyarsa Ta Manchester City Sun Lashe Kofin Capital One A Ingila


Dan wasan tamaula na Najeriya mai shekaru 19 da haihuwa, Kelechi Iheanacho, ya bayyana farin cikinsa a saboda lashe kofinsa na farko a kasar Ingila, bayan da kungiyarsa ta Manchester City ta doke Liverpool a wasan karshe na lashe kofin Capital One.

Sai da aka je ga bugun fenariti kafin a iya tantance zakara a wannan gasa, bayan da aka tashi kunnen doki, aka kuma kara lokaci amma duk da haka ba gwani.

A karshe Manchester City ta lashe wasan da ci 3 da 1, ta samu kofinta na farko a wannan kakar kwallo a Ingila.

Duk da cewa ba a sanya shi cikin fagen kwallon ba, ya zauna kan benchi ne, Iheanacho yace yana alfaharin kasancewa cikin zakarun kofin na Capital One, kuma yana godiya ga dubban magoya bayan da suka zo jinjinawa ‘yan wasan na City.

Iheanacho dan Najeriya ya jefa kwallo a raga a lokacin da Manchester City ta doke Crystal Palace da ci 5 da 1, haka kuma ya jefa kwallo a raga a lokacin da suka doke Hull City da ci 4 da 1 a zagaye na biyar na wannan gasa.

A shekarar 2014, Manchester City ta lashe wannan kofi na Capital One, ta kuma bi bayansa da lashe gasar lig ta Firimiya. A bana, har yanzu babu fitaccen gwani a gasar ta Firimiya, kuma har yanzu Manchester City na cikin masu hankoron kofin Zakarun Kulob-Kulob na Turai.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG