Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sandan Najeriya Ya Gina Gidan Marayu


Gidan Marayu
Gidan Marayu

A Najeriya bayanai sun nuna cewa akwai marayu da dama dake rayuwa cikin yanayi na ban tausayi a sakamakon halin da suka sami kansu na rashin iyayen da suka haifaisu.

A halin yanzu dai bayana sun nuna cewa akwai kashi kashi na marayun dake matukar bukatar tallafi a Najeriya.

Ko baya ga kananan yaran da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya akwai ma marayun da iyayensu sun rigamu gidan gaskiya dama wadanda iyayensu mata sun yarda su ne akan titi.

A can gefe guda kuma akwai yaran da iyayensu masu tabin hankalin ne dake gararamba a titi da suke bukatar matukar kulawa daga hukumomin dama duk masu hanlin kulawar.

Hajiya Raliatu Abdullahi shugaban kula da gidan marayu dake karamar hukumar Kontagora, ta ce kafin a bude wannan gidan sukan tafi da marayun zuwa gidajensu domin kula dasu da kuma ci gaba da binciken kokarin samun iyayensu idan ba’a samu ba sai a bada su ga iyayen riko.

XS
SM
MD
LG