Gwajin makami mai linzami da kasar Koriya Ta Arewa ta yi na baya-bayan nan wata babbar barazana ce ga yankin Pacific da ma duniyar baki daya, a cewar kwamandan harkokin soji na NATO.
Koriya Ta Arewar ta gwada harba makami mai linzamin ne daga jirgin karkashin ruwa da daren ranar Jumma'a a kusa da gabar birnin Sinpo mai tashar jirgin ruwa. Bayanai na farko na nuna cewa makamin ya fadi a Tekun Japan, a cewar kwamandan sojin Amurka, wanda ya bi diddigin yadda aka gudanar da gwajin. Kafar labaran Koriya Ta Kudu ta Yonhap ta ce injin din makamin ya kama da wuta, to amma makamin ya tarwatse ne da tazarar kilomita 10 a sararin sama. Irin wannan gwajin da aka yi a watan Afirilun da ya gabata ma bai yi nasara ba.
"Kim Jong Un da gwamnatinsa na cigaba da ingantawa da kuma gwajin makamai masu linzami, kuma bayan duk wani gwaji su kan kara ingantawa, su na warware matsalolin baya," a cewar babban kwamandan NATO, Janar din Amurka Curtis M Scaparrotti mai kula da bangaren Turai, a hirarsa da 'yan jarida a wuirn babban taron NATO a birnin Warsaw jiya Asabar.