Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Teku Na Iya Mamaye Legas Nan Da 2050 - Dr. Muhtari


Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos
Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos

“Wannan babbar barazana ce da sauyin yanayi ke haifarwa, ya kuma zama dole mu dauki wannan batu da muhimmanci, a kuma samar da matakan da za su kare aukuwar hakan.”

Akwai yiwuwar ruwa ya mamaye birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya nan da shekarar 2050, idan ruwan teku ya ci gaba da tashi yadda ake gani.

Shugaban gidauniyar lura da halittun kasa na Najeriya (NCF) Dr. Muhtari Aminu Kano ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a farkon makon nan.

“Bayan bincike mai zurfi da masana kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya suka yi kan sauyin yanayi, sun bayyana cewa akwai yiwuwar ruwan tekun a Duniya ya taso da takin mita daya nan da tsakanin 2030 da 2050.” Inji Dr Muhtari.

Binciken a cewar Dr. Muhtari, ya nuna cewa ba wai jihar Legas kadai abin zai shafa ba, “har da sauran birane da ke gabar teku a duk fadin Duniya, wadanda doron kasarsu ya gaza takin mita daya da zurfin ruwan tekun.”

Shugaban hukumar ta NCF, ya kara da cewa, dalilin yiwuwar aukuwar hakan, shi ne irin aikace-aikacen da aka yi a gabar tekunan Duniya.

Sannan ya ce, sauyin yanayi ma, na tasiri matuka kan wannan al’amarin.

“Wannan babbar barazana ce da sauyin yanayi ke haifarwa, ya kuma zama dole mu dauki wannan batu da muhimmanci, a kuma samar da matakan da za su kare aukuwar hakan.”

A cewar Dr. Muhtari, “wannan ba matsala ba ce da ta shafi Legas kadai a matsayinta na jiha, matsala ce da ta shafi Najeriya baki daya wacce ke bukatar gwamnatin tarayya ta sa hannu.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG