Kayan na kimanin Naira miliyan dari uku sun hada da siminti da kwanun jinka da kusoshi, da shinkafa da sauran kayan abinci.
Yayinda yake rarraba kayan wa al'ummomin yankunan da lamarin ya shafa gwamnan jihar Alhaji Umaru Tanko Al-Makura yace gwamnati ta dauki matakin sake waiwayar wadanda bala'in rikicin manoma da makiyaya da tashin hankali tsakanin kabilu da al'ummomi daban daban da kuma ambaliyar ruwa da ya sanya wasu da dama rasa muhallansu da dukiyoyinsu.
Gwamnan yace kauyuka da garuruwa sun shiga fama da kone-kone da kashe-kashe sanadiyar rigingimu dalili ke nan da a koyaushe ya kan taimaka masu domin su sake sabuwar rayuwa. Yace amma wannan tallafin ya banbanta da na shekarun baya saboda suna son su tabbatar cewa mutanen da abun ya fi shafa tallafin ya kai garesu.. Yace sun lura cewa akwai gine-gine da dama da walau an konesu ko an rusasu ko kuma ruwa ya kwashesu.Kauyuka da garuruwa 85 ne za'a raba ma kayan.
Wasu da suka anfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum