Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Niger: Ambaliyan Ruwa Ya Rutsa Da Mutane Uku - 42'


 Ambaliyan Ruwa a Niger
Ambaliyan Ruwa a Niger

Ambaliyan ruwa da ya auku a kauyen Tabelot dake cikin yankin Agadez ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku inda har yanzu an ga gawarwaki biyu amma ba'a ga daya ba tare da motar da ta nutse.

A jamhuriyar Niger wasu mutane 3 da suka hada da wata jami’ar kiwon lafiya da wani maras lafiya da dan rakiyarsa sun rasu a kauyen TABELOT dake yankin AGADEZ bayan da ruwa ya yi awon gaba da motar ambulance dinsu lokacin da suka yi kasadar ketara fadamar TELWA a wani lokacin da ruwa ke kwarara da karfin gaske.

Kawo yanzu an gano gawar mutane biyu yayinda ake ci gaba da neman gawar jami’ar kiwon lafiyar da motar da ta rutsa da ita kamar yadda ministan kiwon lafiyar al’uma Dr. Iliyasu Idi Mainasara ya shaidawa Sashen Hausa.

Dr Mainasara ya ce direban ne ya yi ganganci saboda ko da suka kawo bakin gadar ambaliyan ruwan ya soma. Maimakon ya tsaya sai ya shiga domin yana gnin motarsu na da karfi za ta wuce. Kafin ya ankara karfin ruwan ya fi na motar.

A saurari rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:42 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG