Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Najeriya Jihar Oyo ta Kama Motoci dake Dauke da Makamai da Awaki


Rundunar 'Yansandan Najeriya.
Rundunar 'Yansandan Najeriya.

Rundunar 'yansandan jihar Oyo ta cafke motoci fiye da arba'in dake dauke da makamai da awaki.

Shugaban 'yansandan ya fadawa wakilin Muryar Amurka cewa cikin wata daya da ya wuce Allah ya basu nasarori da yawa.

Yace sun kama motoci fiye da arba'in wadan da 'yan fashi da makamai suka kwace. Cikin motocin har da bindigogi da wayoyin wuta irin na hukumar lantarki da ma wasu abubuwan da ake hada wuta dasu. Wasu mutane ne suka nado wayoyin daga wani kauye da ake kira Ileido. Da aka tsare wadanda suke dauke da kayan ba su iya bada bayani na zahiri ba. Sabili da haka ana binciken lamarin.

Akan bincike kuma aka kama wasu da awaki 18. A cikin garin Ibadan kuma wasu sun balle wani shago da daddare suka kwashe wayoyin salula sabbi 69. Su ma an kama su.

Nasarar da 'yansandan suka samu tana da nasaba da hadin kan jama'a da rundunar ta samu.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG