Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Za Ta Kara Jami'an Tsaro a Jihar Taraba


Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris
Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris

Biyo bayan tashe-tashen hankula dake aukuwa a jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya,tawagar sufeta janar na yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ta kai ziyara ta musamman zuwa jihar tare da alkawarin kara yawan ‘yan sanda da kuma samar da jirgin sama mai saukar angulu ga rundunar yan sandan jihar.

Yayin wannan ziyarar ta tuntuba, Sifeta Janar na ‘yan sandan Najeriya ya gana da gwamnan jihar Taraba da kuma sarakuna,iyayen al’umma domin bayyana musu irin matakan da rundunar ‘yan sandan kasar ke dauka,domin kawo karshen tashe tashen hankulan dake faruwa a jihar.

Da farko,yayin wannan taro da aka yi a gidan gwamnatin jihar Sufeta Janar na ‘yan sandan, Ibrahim Idris,ya ce,don shawo kan lamarin yasa za’a karawa jihar karin ‘yan sanda rukuni takwas da za’a tura su yankunan da ake yawaitar samun tashin hankali,baya ga ‘yan sandan kwantar da tarzoman da tun farko aka karo.

Haka nan ma kuma sufeta Janar na ‘yan sandan,ya yiwa al’umman jihar Taraban albishir na samar da wani jirgin sama mai saukar angulu da zai dinga shawagi don zakulo abubuwan dake faruwa domin daukan matakin gaggawa.

‘’Kamar yadda aka sani ne jami’an tsaro na nasu kokari,kuma zamu karo rukuni takwas na ‘yan sanda,baya ga ‘yan sandan kwantar da tarzoman da tun farko aka turo.

‘’Ba zamu yi kasa a gwuiwa ba wajen dakile tashe tashen hankulan dake faruwa a jihar nan,kuma yanzu haka akwai wani jirgin sama mai saukar angulu na ‘yan sanda da aka baiwa jihar nan domin zagayawa, domin samun bayanai,kuma a shirye muke don magance tashe tashen hankulan, inji Ibrahim Idris.

Tun farko ma dai gwamnan jihar Taraban,Arc. Darius Dickson Isiyaku ya bukaci rundunar ‘yan sandan ne da ta taimaka wajen shawo kan tashen hankulan dake aukuwa a jihar.

‘’Gaskiya mun ji dadi da wannan ziyara domin ko cikin kwanakin nan an samu asarar rayuka,muna fatan kwalliya ta biya kudin sabulu” a cewar gwamnan.

A kullum dai akan zargi wasu jami’an tsaro ne da wuce makadi da rawa. To ko yaya masana ke kallon wannan ziyara a yanzu? Barrister Idris Abdullahi Jalo shine shugaban kwamitin kula da hakkin dan Adam na kungiyar lauyoyin Najeriya,reshen jihar Taraba,ya bayyana cewa zuwan shi nada mahimmanci domin zai karfafa ‘yan sanda gwiwa, kana ya ga abun dake faruwa a jihar da idanunsa.

Barrister Jalo ya kara da cewa akwai mahimmanci shi babban Sufeton ya jawo hankalin ‘yan sanda zargin cewa suna musgunawa wasu kana su kare wasu. Kamata ya yi su yi aikinsu bisa gaskiya ba tare da nuna banbanci ko wani bangaranci ba. A cewarsa dole ‘yan sanda su gujewa son ransu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG