Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Tsaron Amotekun Zata Fara Aiki A Hukumance Nan Da Watan Faburairun 2023


Hukumar Tsaro Ta Amotekun
Hukumar Tsaro Ta Amotekun

A farkon makon nan ne Atoji Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Ekiti, Mr. Wale Fapounda ya gabatar da kudirin doka kan kungiyar tsaro ta Amotekun ta yankin Kudu maso yamma ga gwamnan jihar Dr. Kayode Fayemi.

Ana sa ran za a shirya irin wannan kudirin doka a jihohi biyar na yankin Kudu maso yammacin Najeriya domin tabbatar da su a majalisun jihohin, matakin da zai halatta wannan kungiyar ta tsaro.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa, Antoni janar din ya ce kudirin na Ekiti, yana bada shawara ne a kan kafa kungiyar tsaro a jihar Ekiti, wanda aka fi sani da “Rundunar Amotekun”.

Wannan runduna zata taimaka wurin kiyaye doka da oda a jihar Eikiti.

Hukumar Tsaro Ta Amotekun
Hukumar Tsaro Ta Amotekun

Cikin makwakanni biyu da suka wuce, Antoni janar-janar daga jihohi shida suna aiki gadan gadan domin bullo da dokar yin aiki tare na samar da rundunar tsaro ta bai daya.

Da yake amsar kudurin dokar, Gwamna Fayemi ya ce za a tabbatar da dokar Amotekun ya zuwa ranar Juma’a 14 ga watan Faburairu, a jihohi shida dake yankin.

Ya ce sharawar samar da doka kan Amotekun, na daya daga cikin sakamakon ganawar da gwamnonin Kudu maso yamma guda shida, da ministan shari’a, Abubakar Malami da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, suka yi, inda aka amince da cewa sai an fara sanya wasu tsare-tsare na shari’a da suka dace.

Fayemi ya fusata kan yadda ake karkatar da kyakkyawar niyya ta aikin Amotekun da kuma fassara shi a wasu hanyoyi da basu dace ba.

Hukumar Tsaro Ta Amotekun
Hukumar Tsaro Ta Amotekun

Ya yi watsi da rade-radin cewa ana son kafa Amotekun ne domin aiwatar da wasu muradu na yanki ko na daidaikun mutane.

“Mutane da dama sun yi kuskuren fahimtar abin da shirin Amotekun ke nufi”.

Ya kara da cewa, “Ba wata kebantacciyar kariya ga ‘yan asalin yankin kadai, amma don kare lafiyar kowane dan kasa da mazauna jihohi shida, ba tare da la’akari da inda suka fito ba, kuma muddin suna zaune a bisa doka kuma suna mutunta dokar kasar. Yana cikin hurumin mu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi."

Bisa ga cewar Atoji Janar din, Amotekun wani yunkuri ne na hadin gwiwa ga shirin aikin ‘yan sanda unguwa na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

XS
SM
MD
LG