Shelkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta fara binciken zargin da
ake wa jami'an ta, na kashe wasu fararen hula biyu a jihar Sokoto. Kakakin
rundunar Iya Kwamando Ibikunle Daramola, ya shaida hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, cewa rundunar sojin sama ba zata amince da batun danne hakkin bil adama ko rashin da'a da ya shafi jami'anta ba.
Daramola yace an kaddamar da bincike don fayyace abin da ya faru, da irin rawar da sojojin suka taka, kuma muddin an same su da laifi, to tabbas za a dauki kwararan matakai akan su.
A cewar wani masanin harkar sojin sama, Wing Commander M. Salman, domin irin wannan yanayi aka kafa kotun soji, wacce zata gudanar da shari'a
idan har an sami jami'an da laifi.
Wannan matsalar dai tuni ta fara jan hankalin lauyoyin kare hakkin bil adama, irin su Lauya Yakubu Saleh Bawa, wanda yace zasu sa ido don ganin yadda binciken zai kasance.
A saurari cikakken rahoton wakilin muryar Amurka Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum