Rundunar wacce tsohon Sufeto Janar Ibrahim Idriss ya kafa da kuma ke karbar umarni daga Abuja tayi kaurin suna wajen take hakkin dan Adam.
Kafin yanzu dai F-SARS na karbar umarni ne daga hedkwatar rundunar ‘yan sandan kasar, da a baya har zangar zangar lumana ‘yan Najeriya suka yi don neman a soketa, bisa zargin cin zarafin jama'a, al'amarin da yasa mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbsjo lokacin da yake rikon mukamin shugabancin kasar ya bada umarnin ayi mata gyaran fuska.
Daga yanzu dai an soke wannan bangare na ‘yan sanda a matakin tarayya don haka an maidasu karkashin kwamishinonin ‘yan sanda ba jihohi.
Sufeto janar na ‘yan sandan ya yi gargadin cewa duk wani cin zali, sakaci ko ganganci da aka samu wannan runduna da aikatawa to za a dora alhakin hakan ne a wuyan kwamishinan ‘yan sandan da hakan ya faru a jiharsa ne.
Tuni dai masu fafutuka irin su Barrister Yakubu Sale Bawa suka yi marahaba da wannan mataki, inda suka bayyanashi da cewa zai taimaka wajen rage cin mutuncin jama'a da ake yi.
Ga dai Hassan Maina Kaina da karin bayani a cikin wannan rahoto:
Facebook Forum