Shugaban Najeriya ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa a jihar Borno yayin da zabe ke ci gaba da karatowa.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan gobe na Fabrairu.
Yayin ganganmin yakin neman zaben, Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ke neman wa’adi na biyu karkashin jam’iyar APC, ya yi alkwarin zai ci gaba da tabbatar da tsaro a jihar ta Borno, wacce take fama da hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram.
“Alkawarin da muka yi shekara hudu da suka wuce, na zaman lafiya da watada da kuma magance cin hanci da rashawa, da yaddar Allah ku kuka yi sheda akan mun yi nasara akan na farko.” shugaba Buhari ya ce.
Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, “amma da sauran aiki, za mu kuma ci gaba da yi.”
Yayin da yake nasa jawabin, gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya yi alkawarin cewa, jihar Borno ba za ta zamo kashin baya ba wajen samar da kuri’u ga shugaba Buhari.
“Ranar 16 ga watan Fabrairu insha Allahu, idan ba mu zo na daya ba insha Allah za mu zo na biyu a baka kuri’u a kasar nan.” Shettima ya ce.
Prof. Babagana Ummaru Zulum shi ne mutumin da Buhari ya daga hannunsa a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyar APC a jihar ta Borno.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri: