Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rudani na Neman Kunno Kai a Majalisar Dattawan Najeriya


Takaddama akan zaben arewacin Najeriya.
Takaddama akan zaben arewacin Najeriya.

Takaddama akan matakan da ake dauka na magance matsalar tsaro a Arewa maso gabashin Najeriya.

Wani rudani na neman kunno kai a majalisar dattawan Najeriya game da kaddamar da yaki da ‘yan ta’adda da ke ta mamaye da kuma kafa tutocinsu a yankunan arewa maso gabashin kasar.

Sabon kudirin dai na fuskantar fassara da ban-da-ban daga ‘yan adawa, har ma wasu na gannin cewa an kauce ma batun tsaro an koma ga shirin zaben shekarar 2015.

Abu Ibrahim dan jam’iyyar APC ta jihar Katsina, kuma mataimakin mai tsawatarwa a majalisar ta dattawa yace, ana tattaunawa ne akan shawarwarin da ya kamata a gabatar gaban shugaban kasa. Wadanda suka hada da abinda ya kamata a yi idan ana yaki, amma ba a kai ga samun wata matsaya ba tukunna, balle ma ace an hana zabe. Har ma Abu Ibrahim ya ambaci cewa shugaban majalisar yace ta batun zabe ake ba Yanzu, ta tsaro ake.

Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>

A bangaren ‘yan majalisar dattawan da suka fito daga yankunan gabas, sun yi ma batun wata fassara ta daban, cewaana so a hada baki da mahukunta da masu ruwa da tsaki ne kawai a hana zabe a yankin. Shi ko Alkali Jajere daga jihar Yobe, cewa yayi babu gudu ba ja da baya akan batun zabe, don kuwa ‘yan yankin zasu yi zabe.

Kamar yadda zaku ji anan, karin bayani daga Madina Dauda

Shi kuma Abdul Ningi Mataimakin shugaban masu rinjaye ta majalisar yace, batun bai saba ma kundin tsarin mulkin kasar ba balle kuma na masu nazarin sa. A cewar Abdul Ningi, duk masu fadin ba a isa a hanasu zabe ba sun nuna cewa basu san darajar rayuwar dan’adam ba, ko kuma suna so suce yakin da akeyi ba yaki bane?

Wannan takun saka dai na nuna alamar cewa majalisar na shirin fuskantar wani sabon yanayi ko bayan ganawa da shugaban kasa Goodluck Jonathan. Abin da ya jawo hankalin Adullahi Garba Mohammed tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar AD, inda ya bada shawara da a jawo hankalin masu mulki su gane cewa ya kamata a yi harkar dimokradyyya yadda ‘yan kasar zasu ga cewa suna da hakki a ciki. Bugu da kari kasashen duniya suma su san cewa Najeriya tayi karfi, kuma dimokradiyyar kasar ta zama abin koyi ga duniya.

Ganin yadda batun ke kawo rarrabuwar kai, Dr Lanre Adebayo shugaban cibiyar nazari da koyar da harkokin dimokradiyya da ke Abuja, ya yi kira ga shugabanin Najeriya da su hada kawunansu, su kuma kauce ma bambancin addini ko siyasa domin su kawo karshen ta’addanci a kasar. Don ga dukan alamu batun na shirin shiga halin kaka-na-kayi a dandalin siyasar kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG