Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashar Muryar Amurka ta cika shekaru 70 da kafawa


Bukin cika shekaru 70 da kafa VOA.
Bukin cika shekaru 70 da kafa VOA.

Shugaban Amurka Barack Obama da sauran manyan shugabannin duniya sun shiga sahun masu taya Muryar Amurka murnar bukin cika shekaru 70 da kafa tashar

Shugaban Amurka Barack Obama da sauran manyan shugabannin duniya sun shiga sahun masu taya Muryar Amurka murnar bukin cika shekaru 70 da kafa tashar tare da aikawa da sakonnin fatar alheri.

Shugaba Obama ya yabawa Muryar Amurka sabili da bada labarai sahihai a lokacin da gwamnatocin kasashen ketare suke hana daukar labarai da kuma shugabannin da suke tauye yancin da ya wajaba ga kowanne bil’adama. A cikin sakonshi ta bidiyo da aka yayata a ranar bukin da aka yi jiya Laraba, shugaba Obama yace Amurka ta kara karfi yayinda kuma ake kara samun adalci a kasashen duniya sabili da kokarin Muryar Amurka.

A nata sakon fatar alherin, shugabar rajin damokaradiya ta Bama Aung San Suu Kyi tace bukin cika shekaru 70 da kafa Muryar Amurka tamkar bukin cika shekarun babban abokinta ne. Bisa ga cewarta Muryar Amurka da sauran tashoshin watsa shirye- shirye sune abokan da suka taya ta hira a tsawon shekarun da take daurin talala.

Shugabannin addinin Tibet Dalai Lama yace sashen Tibet na Muryar Amurka ya taka gagarumar rawa a rayuwar mutanen Tibet ta wajen watsa labarai sahihai, bisa ga cewarshi , ya hakikanta cewa, kafofin watsa labarai kamar Muryar Amurka suna da muhimmanci kwarai.

Tashar Muryar Amurka da gwamnatin Amurka ta kafa lokacin yakin duniya na biyu domin watsa labarai a yankunan da sojojin Hitila suka mamaye, ta zama babbar tashar dake watsa labarai a harsuna arba’in ga kimanin mutane miliyan 140 kowanne mako.

Shugaban Amurka Barack Obama

Muryar Amurka ta watsa shirinta na farko ne cikin harshen Jamusanci ranar daya ga watan Fabrairu a shekara ta dubu da dari tara da arba’in da biyu da kalmomin farko “Ga Murya daga Amurka tana magana”- (“Here speaks a voice from America”). Aka ci gaba da watsa cewa “ Yana yiwuwa labarin ya yi dadi. Yana yiwuwa labarin bashi da dadi. Zamu gaya maku gaskiya.”.

Ana watsa shirye- shiryen Muryar Amurka a talabijin da radiyo da hanyar sadarwar intanet da wayoyin salula, tare da hadin guiwa da sama da tashohi dubu daya da dari biyu a kasashen duniya. Banda sama da ma’aikata dubu daya da dari daya dake birnin Washingon, Muryar Amurka tana aiki da manema labarai a kasashen duniya da ake fama da tashin hankali. Farkon wannan shekarar kungiyar Taliban ta dauki alhakin kashe wani dan jarida dake yiwa Muryar Amurka aiki a Pakistan

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG