Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Sudan: Wata Sabuwar Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Za Ta Fara Aiki


FILE - Volker Perthes, Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan.
FILE - Volker Perthes, Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan.

Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya yi marhabin da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka da Saudiyya suka jagoranta da ke shirin fara aiki, duk da cewa rikicin Sudan bai nuna wata alama ta ja baya ba.

Volker Perthes ya shaida wa taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, "Wannan wani ci gaba ne na marhabin, ko da yake an ci gaba da gwabza fada da yunkurin sojoji har zuwa yanzu, duk da kudurin da bangarorin biyu suka yi na ba za su ci gaba da fada ba kafin tsagaita wutar ta fara aiki."

Perthes ya yi tafiya zuwa New York daga Port Sudan. Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da wasu ma'aikatanta da ayyukanta na wani dan lokaci zuwa birnin na Red Sea, bayan kazamin fada da ya barke a babban birnin kasar Khartoum, a ranar 15 ga watan Afrilu.

Yarjejeniyar tsagaita wuta mai dauke da sa hannun hafsan hafsoshin sojin kasar Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun kungiyar sa kai karkashin jagorancin Janar Mohamed Dagalo, za ta fara aiki da karfe 9:45 na dare. lokacin yankin a ranar Litinin, kuma yana daukar tsawon kwanaki bakwai, wanda bangarorin zasu iya sabunta ta.

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada a lokacin tsagaita wuta da aka yi a baya, an amince da wannan a yayin gudanar da shawarwari a hukumance a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, kuma zai hada da tsarin sanya ido da ya kunshi wakilai uku daga Saudiyya da Amurkawa da kuma sojojin Sudan biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG