Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadan Sudan Ya Hana Kananan Yara Samun Ilimi - UNICEF


FILE - Kananan yara daga cikin yan gudun hijirar Sudan ke wasa.
FILE - Kananan yara daga cikin yan gudun hijirar Sudan ke wasa.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yakin Sudan ya raba akalla yara 450,000 da gidajensu, tare da haddasa gudun hijira zuwa kasashe makwabta.

Kungiyoyin ba da agaji sun ce ana hana wadannan yaran ‘yan gudun hijira ilimi, tare da fuskantar hatsarin fadawa hannun ba ta gari, kamar auren yara ko daukar makami don shiga kungiyar ‘yan bindiga.

Yayin da dubun dubatan ‘yan gudun hijira ke isa kan iyakar Sudan zuwa Chadi, yawancin taimakon da Majalisar Dinkin Duniya ke bayarwa da kungiyoyin agaji ya mayar da hankali ne kan ruwa da abinci da kuma sauran kayan amfani na yau da kullun ga ‘yan gudun hijira.

Amma 'yan gudun hijira kamar Abdelnasser Mahamout mai shekaru 18 da haihuwa, sun ce akwai matukar bukatar ilimi. Yakin basasar Sudan, wanda ya fara a ranar 15 ga Afrilu, ya haifar da rikicin kabilanci a yammacin Darfur.

Dole ta sa ya gudu zuwa Chadi ba tare da iyayensa ba.

Mahamout ya ce tun makonni bai ji daga iyayensa ba, kuma bashi da masaniyar suna raye ko sun mutu.

Yanzu haka yana zaune a wani karamin sansani tare da ’yan uwansa, kuma ya ce babu wata hanya da zai iya daukar jarrabawar shiga jami’ar Sudan.

Malek Mohammed, malami da ya yi gudun hijira zuwa kasar Chadi daga yammacin Darfur, ya koka da halin kunci da yaran da ya ke koyarwa a baya suke zama a ciki.

Mohammed ya ce malamai na kokarin samar da hanyar da yara za su yi jarrabawar Sudan a Chadi.

Gwamnati a Khartoum ta daina aiki tun lokacin da aka fara yakin basasa, don haka da alama ba za a iya daidaitawa ba.

Education Cannot Wait, ECW, ita ce asusun Majalisar Dinkin Duniya don ilimi a lokutan rikici. Daraktar kungiyar, Yasmine Sherif, ta kai ziyara kasar Chadi a watan Mayu, inda ta yi alkawarin baiwa kasar Chadi dala miliyan uku domin samar da ilimi.

Tasirin yakin Sudan kan yara bai takaita ga ilimi ba kadai. Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar 12 ga watan Mayu cewa, wata masana'anta ta Sudan da ke samar da kashi 60 cikin 100 na abinci na musamman da ake amfani da su wajen magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar an lalata su saboda fadan.

Dubun dubatar yara a Sudan ne za su samu kansu cikin irin wannan hali.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG